Ranar Dimokuraɗiyya: Fintiri Ya Saki Fursunoni 6 Da Aka Yanke Wa Hukunci
Gwamnan Jahar Adamawa Ahmadu Fintiri ya saki masu laifi 6 da aka yanke wa hukunci dake a cibiyar gyaran Akidu guda 5 dake faɗin Jahar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a matsayin bikin ranar Dimokuraɗiyya ta ranar 12 ga watan yunin, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana daga Gwamnatin Jahar, dake Yola.
Sanarwar mai ɗauke dasa hannun Sakataren Ƴan Jarida Humwashi Wonosikou ya fitar, yace Gwamnan yayi haka ne, kamar yadda sashe na 1
212(i)(b) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bashi iko.
Wonosikou ya ƙara dacewa Gwamna Fintiri ya hana hukuncin kisa da aka yanke wa, wani zuwa zaman kaso na tsawon rayuwar sa.
Yace Bursunonin sun kasance suna zama a cibiyoyin gyaran Aƙidu na tsohuwar Yola, da Jada, da Numan, da Mubi, da Jimeta.
Sakataren Harkokin Ƴan Jarida na Gwamnan yace , Fintiri ya yi haka ne, bayan shawara da Majalisar kula da Afuwa ta bayar, domin rage cunkoson Gidajen Gyaran Aƙidu na Najeriya, domin bikin ranar Dimokuraɗiyya.