Ƴan Sanda Sun Kama Mafarauta 3 Da Laifin Garkuwa Da Mutane A Jahar Adamawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu mafarauta guda uku da wasu da ake zargi da hada baki wajen taimakawa masu garkuwa da mutane a kananan hukumomin Girei da Fufore a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Sulaan Nguroje, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce wadanda ake zargin: Auwal Mohammed mai shekaru (28), Isa Umaru (40), da Rabiu Mohammed (19) sun addabi kauyukan Pariya Daware da Girei.

Ya ce rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar kwato babur daya, bindigogin gida da sauran kayayyaki daga hannun wadanda ake zargin.

“Bincike ya zuwa yanzu ya nuna cewa wadanda ake zargin sun ci amanar amincewar al’umma da aka ba su na kare rayuka da dukiyoyi, sun ci gaba da samar da kayayyakin abinci da sauran bukatun yau da kullum ga ‘yan uwansu masu garkuwa da mutane a kewayen yankin,” in ji sanarwar.

Kazalika yace ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin kuma za’a gurfanar dasu a gaban kotu da zarar an kammala bincike

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram