Adeyanju Ya Bayyana Dalilan Da Zai Sanya Kwankwaso, Peter Zasu Iya Kayar Da Tinubu, Atiku

Gabanin zaben 2023, an gargadi ‘yan takarar shugaban kasa irin su Peter Obi, Rabiu Kwankwaso, Omoyele Sowore da sauran ‘yan siyasa kan dalilin da ya sa ba za su iya kayar da jam’iyyar APC, da PDP, ba.

Lauyan mai fafutuka, Deji Adeyanju, ya ce Obi, Kwankwaso, Sowore, da sauransu ba za su iya kayar da Bola Tinubu da Atiku Abubakar ba idan ba su yi aiki tare ba.

Adeyanju ya yi gargadin cewa a yankunan karkara ake cin zabe ba a birane ba.

A cikin jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na twitter, mai sharhin zamantakewa da siyasa ya ce ya kamata ‘yan siyasa su hadiye girman kai su yi aiki tare.

A cewar Adeyanju: “Ba yadda za a yi Peter Obi, Kwankwaso, Sowore da sauran ’yan siyasa su kayar da APC da PDP idan basu hada kai ba saboda ba a ci zabe a birane ba, sai a karkara.

“Ya kamata ‘yan siyasa su koyi hadiye girman kai su yi aiki tare.

“Wannan dole ne in zama shugaban kasa ta kowane hali shi ya sa APC da PDP za su ci gaba da kaskantar da ‘yan siyasa masu girman kai.

“Ku rungumi wannan gaskiyar don amfanin ‘yan Najeriya kuma ku yi aiki tare

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram