Tsohon gwamnan jahar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar PDP Barista Ibrahim Shema ya ce babu abinda mulkin APC ya haifar a Najeriya sai talauta jama’a
Focus News Hausa ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan ya ce mutane ma su sana’o’i jarinsu ya wargaje, yunwa da fatara sun dami al’umma a cikin ƙasar.
Shema ya ci gaba da cewa, matsalar rashin tsaro ta zama ta addabi ko wane ɓangare a Najeriya.
Sai dai ya ƙara da cewa Allah ba ya kuskure don haka Allah ya yi haka ne domin al’umma su fahimci wacece APC da mutanen cikinta.