Ƙungiyar Musulmi MURIC Ta Buƙaci Atiku Da Kada Ya Ɗauki Wike Abokin Takarar Sa

Ƙungiyar Kula da Haƙƙokin Musulmi (MURIC) ta shawarci Alhaji Atiku Abubakar, Ɗan Takarar Jam’iyyar PDP akan ɗaukar Nyesom Wike, Gwamnan Jahar Rivers a matsayin Abokin Takarar sa.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan MURIC Farfesa Ishaq Akintola ya sanyawa hannu aka fitar wa Manema labaru a ranar 14 ga watan yunin Shekarar 2022.

“Wike yana ɗaya daga cikin Kiristoci masu tsatstsauran ra’ayi” da musulmi suka yi mashi baƙin fenti,” Inji Sanarwar.

Sanarwar tace “yazo mana cewa Gwamna Nyesom Wike na ɗaya daga cikin waɗanda ake ganin za’a ɗauka a matsayin Abokin Takara na Jam’iyyar PDP na Alhaji Atiku Abubakar. Munga ya zama dole mu bada shawara akan haka, Wike ya kasance wanda baya Son musulmi, mai rushe Masallaci.

“Tsatstsauran ra’ayin Wike yana nan a kundin bayanan mu. Ya ayyana Jahar Rivers a matsayin ta Kiristoci, wanda ya saɓawa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya. Bamu da tabbacin cewa idan ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa bazai yi abinda yafi haka? Bai kamata Wike ya riƙe muƙami ko guda ɗaya ne a matakin Tarayya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram