Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari
Yan Bindiga sun Kashe wata daliba Mai zana Jarabawar fita daga Sakandire a Makarantar St. Monica Girls Secondary School dake Otukpo Jahar Benue.
Rahoto ya bayyana cewa, an Kashe Ɗalibar ne bayan taje ɗauke kayayyakin sanya wa data shanya domin su bushe.
Dalibar An Kashe ya ne alokacin da take rubuta Jarabawar kammala sakandiri.
“Yarinyar Daliba ce a Makarantar Sakandare ta yanmata ta St. Monica Girls dake Otukpo, kuma tana zaune da iyayen ta a gida mai lamba 38 kan hanyar Idikwu.
“Yan bindigar guda biyu sun hauro katanga ne sun Kashe yarinyar bayan ta wanke kayan Makarantar nata ta shanya”, Inji Majiya
Lamarin ya faru ne, a gaban Yar uwar mamaciyar Mai suna Rosemary, daga bisani ta ta ruga domin sanar da mahaifin nasu abinda ke faruwa.
Yan Bindigar sun bar gidan bayan sunyi nasarar kashe Yarinyar.
Mai Magana da Yawun Rundunar Yan Sanda Ta Jahar, SP Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta kuma Kara da cewa lamarin ya faru ne a ranar juma’ar da ta gabata.