Dalilan Da Suka Sanya Buhari Ya Gana Da Gwamnonin APC A Villa

Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata yayi ganawar sirri da Gwamnoni a Karkashin jam’iyyar APC, a fadar sa dake Villa Abuja.

Duk da Gwamnonin sun ki jawabi ga manema labarai akan taron, amma an tabbatar da cewa yana da nasaba da fitar da Abokin Takarar Bola Tinubu.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar, kuma Gwamnan Jahar Kebbi, Atiku Bagudu ya jagoranci Gwamnonin ya zuwa ga taron.

Tun bayan samun nasarar da Tinubu ya samu a ranar Laraba amatsayin Ɗan takarar Jam’iyyar yake kan matsi na fitar da wanda zai kasance Abokin takarar sa.

Ɗan Takarar Jam’iyyar APC ya Kasance yana tuntuɓar masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar, wanda akwai yiwuwar yin takarar musulmi da Musulmi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram