Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya tayi gargaɗin ladabtar da Jami’o’in da suka kasa bin hukuncin da ta yanke aka yajin aiki, a yayinda take cigaba da tattaunawa da Gwamnatin Tarayya.
Shugaban Ƙungiyar ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a Najeriya a ranar Litinin a Abuja.
ASUU ta kasance tana Yajin aiki na tsawon watanni 5 domin neman a biya mata buƙatun ta.
Malaman Jami’o’in sun shiga Yajin Aiki da suka haɗa da kuɗaɗen tafiyar da harkokin Gwamnati, da Kuɗin Alawus-Alawus, da manhajar biyan Albashi ta UTAS.
Sauran sun haɗa da yarjejeniyar ASUU-FG na Shekarar 2009, da rashin dai-dai akan hanyar biyan kuɗi ta IPPIS.
Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya ruwaito cewar tun lokacin da Kungiyar ta shiga Yajin Aiki wasu mambobin ta sun fita daga gare shi domin dawo wa harkokin karatu.
Amma Osodeke yace “zamu hukunta dukkanin waɗanda suka fita daga yajin aikin yanda ya kamata.
“Zamu hukunta su, amma zamu bi hanyar daya kamata. Tuni mun hukunta wasu a tsarin dokar Kungiyar.