Kwankwaso Yace Zai Magance Matsalar Tsaro, Da Inganta Tattalin Arziki
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar NNPP Rabi’u Kwankwaso, yace Gwamnatin da zata magance matsalar tsaro tare da inganta tattalin arziki idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023.
Ya bayyana haka a ranar Litinin a Calabar a lokacin da yake jawabi ga Ɗumbin Magoya Bayan sa, bayan nasarar daya samu a Zaɓen Fidda Gwani.
“Matsalar tsaro da suka haɗa da Ta’addanci, da wasu matsalolin duk za’a magance su,” yana mai ƙara dacewa “zai inganta tattalin arzikin Kasa, kuma NNPP zata tabbatar da haɗin kan Ƙasa”.
Yace Jam’iyyar nada mutane masu daraja, da zasu iya jagorantar Ƙasar, sai ya buƙaci magoya bayan sa dasu samo Katin Ɗan Ƙasa domin Babban Zaɓen Shekara mai zuwa.
Yace Jam’iyyar ta zama Sananniya a dukkanin Ƙananan Hukumomi na Ƙasar.
Tunda Farko, Shugaban Jam’iyyar Tony Odey, ya bayyana Kwankwaso a matsayin wanda yazo domin ceto Ƴan Najeriya.