Yanzu-Yanzu: Masu Ruwa Da Tsaki A APC sun yi Watsi Da Tsarin Takarar musulmi Da Musulmi

Yanzu-Yanzu: Masu Ruwa Da Tsaki A APC sun yi Watsi Da Tsarin Takarar musulmi Da Musulmi

Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC matakin da kasa, da kuma kungiyar gwamnonin jam’iyyar, da sauran manya masu fada aji sun yi watsi da tsarin da ake kokarin fito da shi na shugaban kasa da Mataimakin su kasance musulmai.

Baki dayan su sun goyi bayan muƙamin Mataimakin shugaban kasa ya kasance a yankin arewa, amma kuma a nemi Kirista a bashi.

Da suke magana yayin wani taro da aka shirya dangane da tunawa da ranar Dimokuraɗiyya, shugaban kungiyar masu fada ajin jam’iyyar Aliyu Audu, yayi watsi da tsarin yan takara matakin kasa su kasance musulmai.

A cewar sa hakan babu abinda zai haifar face nadama, domin kuwa zai taka rawa wajen ruguza zaman lafiyar da ake alfahari da shi.

Audu ya kara da cewa tsarin musulmi da kirista abu ne daya taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya a Najeriya.

Don haka ci gaba da wannan tsari shine mafita ga zaman lafiyar kasar, akasin hakan kuwa sai dai ya zama abun kaico.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram