Zaɓen Ekiti: Ku guji Saida Ƙuri’un ku — Wani Lauya Yayi Kira Al’umma
Gabanin Zaben Gwamnan Jahar Ekiti, wani Fitaccen Lauya Morakinyo Ogele ya shawarci masu kaɗa ƙuri’a dasu guji saida ƙuri’un su ga Ƴan Siyasa a ranar Zaɓe.
Ya yi zargin cewa Jam’iyya mai Mulki ta APC tana shirin shigo da sayen ƙuri’u, sai yayi kira ga mutanen Jahar dasu guji hakan.
Yace Jam’iyyar ta gaza kwata-kwata musamman ga Al’ummar Jahar a shekarun ta 4 da suka gabata, kuma bata kamata ta cigaba da kasancewa a Mulki ba.
Lauyan yayi zargin ne a cikin wata budaɗɗiyar takarda ga Al’ummar Jahar Ekiti. Takardar dai an tura ta ga Manema labaru a Akure, Babban Birnin Jahar Ondo a ranar Litinin mai taken “Takarda ga Al’ummar Ekiti.
A cewar sa, Gwamnati mai ci a yanzu ta lalata Jahar, sai ya yi kira ga Al’umma dasu kori APC daga Mulki.
Takardar tace “muna kallo a tsanake muga mike fili a Jahar Ekiti, da yanda ta lalata Jahar. Ba wulaƙanci bane kace Gwamnati a Ekiti bata yi komai ba, wajen gina mulkin ta.