Za a yi Makoki Na Kwanaki 3 A Burkina Faso Kan Kisan Mutane 50

Za a yi Makoki Na Kwanaki 3 A Burkina Faso Kan Kisan Mutane 50

Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da zaman makoki na kwana uku daga yau Talata bayan kashe aƙalla mutum 50 a ƙarshen mako a arewacin ƙasar.

Shugaban mulkin sojan ƙasar Laftanar Kanal Paul-Henri Damiba ne ya bayar da umarnin yin zaman makokin.

A ranar Litinin ne gwamnatin ƙasar ta ce an kashe farar hula 50 a wani hari da wasu yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kai a yankin Seytenga inda gwamnatin ta ce akwai yiwuwar adadin mutanen zai iya ƙaruwa.

Wasu rahotanni sun ce adadin mutanen da suka rasu ya kai zarta 10.

A lokacin zaman makokin, za a rage tsawon tutocin ƙasar a kusan duka gine-ginen gwamnati da kuma ofisoshin jakadancin ƙasar a wasu ƙasashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram