Janar-Sufirtanda na God Mission International Bishop Paul Nwachukwu yace takarar Musulmi da Musulmi a zaɓen Shugaban Ƙasa na Shekarar 2023, kiristoci bazasu taɓa amince wa dashi ba.
Nwachukwu yace manyan Jam’iyyu guda biyu da suka zaɓi musulmi a matsayin Ɗan Takarar su tuna cewa Najeriya ƙasa ce mai Mabambantan ra’ayoyi, da addini.
Yace zaɓen musulmai a matsayin abokanan takarar su, zai haifar da mance kiristoci kenan.
A cikin wata sanarwa mai taken “ina son ƴan Siyasa su tuna cewa Najeriya ƙasa ce mai Mabambantan ra’ayoyi, kuma a wurin ɗaukar abokanan takarar su, baza’a yarda su ƙara ɗaukar wani musulmi ba.
“Najeriya ta kowa da kowa ne, kuma kowane ɓangare da Addini yana da mahimmanci. Zaɓen musulmi a matsayin abokin Takara, zai haifar da mance kiristoci,” Inji Nwachukwu.