Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Jahar Abia

Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Jahar Abia

Wasu Ƴan bindiga a daren ranar Talata sun sace tsohon Wakilin Kamfanin Jaridar Sun Chucks Onuoha daga Umungasi, a garinsa na Ohuhu Umuahia.

A cewar Majiya daga iyalan sa, Onuoha wanda yanzu shine Babban Editan All Facts, an Sace shi da misalin ƙarfe 10 na dare wanda suka bi ta katangar gidan sa.

Majiyoyi sun ce ƴan bindiga sun kuma sace Mota ƙirar Jeep a tare dashi.

Tuni wanda suka sace shi, sun fara tuntuɓar iyalansa, inda suka buƙaci su biya su kuɗin fansa Naira Miliyan 10.

A lokacin da aka tuntuɓe ta, Rundunar Ƴan Sandan Jahar Abia sun ce har yanzu ba’a sanar dasu ba kai tsaye, kan lamarin.

Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Geoffrey Ogbonna yace “har yanzu ba’a sanar damu kai tsaye ba”.

Amma Shugaban Al’ummar Suleiman Anyalewechi ya Tabbatar da faruwar lamarin ga Ƴan Jarida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram