Ku Ƙara Wa’adin Rajistar Zabe da watanni 2 — Ƴan Majalisu sun buƙaci INEC
Majalisar Wakilan Najeriya tayi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC data ƙara wa’adin rajistar Katin Zaɓe daga 30 ga watan yunin Shekarar 2022, zuwa watanni biyu, domin baiwa ƴan Najeriya da suka isa damar rajista, tare da samun Katin Zaɓe nasu na Din-Din-Din domin Babban Zaɓen Shekarar 2023.
Haka zalika, Majalisar ta kuma baiwa Kwamitin ta umarni dasu tattauna da INEC “akan ganowa tare da magance matsalar ƙarancin kayayyakin rajistar Katin Zaɓe da Ma’aikata.
Tattaunawar zata kasance an samu damar aikewa da ƙarin Na’urorin Rajistar Zabe guda 30 a dukkanin Ƙananan Hukumomi 774, ya horas tare da tura Ma’aikata a wuraren yin rajistar, gami da samar da tsaro ga ma’aikatan wucin gadi.
Kwamitin an kuma umarce shi daya dawo da rahoto cikin makonni biyu domin ɗaukar mataki.
Wani Ɗan Jarida Benjamin Kalu a Zaman ta na ranar Laraba ya gabatar da wani Ƙudiri mai suna “buƙatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta data ƙara wa’adin yin rajistar Zaɓe tare da tura Ma’aikata da kayayyakin Zaɓe.