Gobara Ta Laƙume Shaguna 42 A Jami’ar ATBU, Bauchi

Gobara Ta Laƙume Shaguna 42 A Jami’ar ATBU, Bauchi

Kimanin Shaguna 42 dake a cibiyar Dalibai na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi suka lalace, bayan Gobara ta ɓarke, ta laƙume kayayyakin Miliyoyin Nairori.

Rukunin Shagunan na D da suka lalace, suna nan bayan Ɗakunan Kwanan Mata dake a mazaunin Jami’ar na Yelwa.

Shagunan da Gobarar ta lalata sun haɗa dana Inda ake harkokin Kamfuyuta, da Aski, da kayayyakin shaguna.

Gobarar wadda ta fara daga wani shago guda ɗaya, ta faru ne a dalilin wutar lantarki.

Lamarin ya faru ne a farkon safiyar ranar Laraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram