Gwamnatin Legas Tace Ta Shirya Tsaf Domin Kawar Da Sana’ar Acaɓa

Gwamnatin jihar Legas ta kaddamar da rundunar yaki da Okada da za ta bi sahun ‘yan sanda wajen aiwatar da dokar hana aikin a kananan hukumomi shida, da manyan manyan tituna, da gadoji ake jihar.

Kwamishinan Sufuri, Dr. Frederic Oladeinde, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Legas, inda sanarwar ta ce, haramcin ya yi daidai da dokar sake fasalin fannin sufuri na shekarar 2018.

Oladeinde ya ce gwamnati ta shirya tsaf domin karfafa dokar hana Okada a kananan hukumomin shida da kuma manyan garuruwa tara.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da rundunar ta musamman da ake kira Anti-Okada Squad, wadda za ta dunga kai rahotonninta ga rundunar ‘yan sanda .

Sai dai Oladeinde ya bukaci mazauna jihar da su hada kai da gwamnati domin samun nasara a yunkurinta.

Kwamishinan ya sake nanata cewa babura da aka kama za a murkushe su a idon jama’a, domin ya zamo izina gama su karya doka.

Anashi bangaren Babban Sakatare na Ma’aikatar Sufuri, Kamar Olowoshago, ya kuma bukaci jami’an na Anti-Okada da su kasance masu himma da gaskiya wajen gudanar da ayyukansu.

Taron kaddamarwar ya sami halartar kwamishinan gidaje, Fatai Akinderu, wanda daga bisani ya mika takardar shaidar kammala horaswa ga rundunar ta Anti okada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram