Orji Kalu Yace Babu Wata Matsala Takarar Musulmi Da Musulmi
Shugaban Masu Horaswa na Majalisar Dattijan Najeriya Sanata Orji Kalu, yace babu wani matsala idan Jam’iyyar APC tayi tsarin Takarar Musulmi da Musulmi domin Shekarar 2023.
Ana cigaba da samun rikice-rikice kan Mataimakin Shugaban Ƙasa musamman daga addinai domin ganin anyi raba dai-dai.
Ƙungiyoyin Addinai da suka haɗa da Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya, da Ƙungiyar Katolika ta Najeriya sun gargaɗi Ƴan Jam’iyyu akan bada tikitin Takara ga Musulmi da Musulmi a Zaɓen Shugaban Ƙasa na Shekarar 2023.
Amma a jawabin sa, Kalu a lokacin da yake yiwa ƴan Jarida Jawabi a Majalisar Dattija a ranar Laraba, ya shaidawa Kiristoci cewa babu wata matsala daya kama ta aji domin Matar Bola Tinubu Fasto ce, wadda a kowane lokaci zata kasance tana son addinin ta.
Yace “Idan da ace ina a muƙamin Ahmed Tinubu, Matar sa Babbar Fasto ce. Zan je ayi Tikitin Musulmi da Musulmi. Abinda yafi mahimmanci shine Jam’iyyar ta samu nasara. Dole mu daina wannan shirmen akan Addini.
Ya kara da cewa ba maganar addinin mutum ya kamata ayi .