Zamfara: Zamu Katse Layukan Sadarwa Domin Ceto Wanda Aka Sace – Matawalle

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya tabbatar wa mazauna jihar cewa za a kubutar da duk wadanda aka sace a jihar.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Zailani Bappa ya fitar, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta dauki matakin kawar da matsalar tsaro a jihar.

Gwamnan ya kuma yi kira ga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su da su kasance da kwarin guiwa kan yadda gwamnatin jihar za ta iya dakile ‘yan fashi a da suka addabi jihar

“Wannan lamari na musamman ya nuna wani lokaci na bakin ciki a yakin da ake yi da kalubalen tsaro da muke fuskanta a jiharmu mai daraja.”

“Ina kira ga iyalan duk wadanda aka sace da su amince da kwarewar mu na yin duk abin da ya kamata a yi wajen kubutar da ‘yan uwansu.

“Na umarci dukkan hukumomin tsaro da su gaggauta gano mutanen da aka sace kuma in sha Allahu za a ceto su.”

Matawalle ya kuma ce gwamnatin jihar ba za ta amince da duk wani aiki na rashin da’a daga wasu marasa kishin kasa da ke son yin amfani da halin da ake ciki a yanzu don cin ma manufofin siyasar su ba.

“Mu gwamnati ce mai alhakin kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaron lafiyar dukkan ‘yan kasarmu a kowane lokaci. Ba za mu lamunci zagon kasa ko cin mutunci na siyasa da cin zarafin wasu ba, wanda zai iya kawo cikas ga rashin tsaro a jiharmu,” in ji Matawalle.

“Mun lura da karuwar ayyukan masu ba da labari wanda ke haifar da hare-haren ‘yan bindiga da yawa a kan wurare daban daban. Za mu dauki tsauraran matakai don magance halin da ake ciki yanzu, gami da yiwuwar rufe hanyoyin sadarwa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram