Ƴan Sandan Anambra Sun Kama Matashi Mai Shekaru 34 Da Laifin Kashe Yarinya

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta ce ta kama wani mutum mai shekaru 34, Mista Onwele Anayo da laifin kashe wata yarinya ‘yar shekara uku mai suna Divine Eze, a rukunin gidaje na Hillview Estate, dake Nkwelle -Ezunaka, karamar hukumar Oyi ta jihar Anambra.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Ikenga Tochukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Alhamis a Awka babban birnin jihar Anambra.

Ya ce, “Jami’an ‘yan sandan jihar Anambra a yau 16/6/2022 sun kama wani Mista Onwele Anayo ‘M’ mai shekaru 34 a duniya kan kisan Divine Eze ‘M’ mai shekaru 3, da ke zaune a rukunin gidaje na Hillview Estate, Nkwelle -Ezunaka.

“Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya ziyarci mahaifin wadda aka kashe a ranar Laraba 15/6/2022 kuma ya kwana a gidan wanda aka kashe. Da sanyin safiyar ranar Alhamis 16/6/2022 ne rikici ya barke tsakanin mahaifin da wanda ake zargin.

“Wanda ake zargin (Mr Anayo) ya yi amfani da lokacin da take barci ya kashe ta, ta hanyar buga ta da kasa. Mista Anayo, ya dauko wuka daga dakin, ya bi mahaifin yarinyar har wajan gidan, inda yayi barazanar kashe shi.

Jami’an ‘yan sanda sun ziyarci inda lamarin ya faru inda suka zakulo gawar yaron kuma ana ci gaba da gudanar da bincike. Za a sanar da ƙarin bayani a nan gaba”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram