Duk Ɗan Siyasar Da Ke Son In Zaɓe Shi A 2023 Sai Dai Mu Yi Tsada Da Shi Ya Sayi Ƙuri’ata – Okon Lagos

Daga Maryam Salisu Batsari

Sau Ɗaya Tal Ƴan Siyasa Ke Ziyarar Masu Zaɓe A Cikin Shekaru 4 Don Haka
Sai Na Zaɓa Na Tarje Farashin Da Zan Sayar Da Ƙuri’ata A 2023 – Okon Lagos

Jarumin shirya fina- finan turanci na Ƙamfanin Nollywood, Okon Lagos, ya bayyana cewa, zai sayar da kuri’arsa a yayin babban zaben shekarar 2023 Mai zuwa.

Jarimin ya bayyana cewa zai sayar da kuri’ar tasa akan farashi mai tsada saboda yan siyasar Najeriya na ziyartar Al’umarsu sau ɗaya kacal acikin shekaru huɗu.

Jarumin ya ce shi fa duk abinda za’a fada game da cewa kada mutum ya sayar da kuri’arsa ba zai yi wani tasiri gare shi, ya ce yana da Katin zabensa kuma zai saida kuri’arshi akan farashin da ya dace.

Okon ya ci gaba da cewa, an san cewa, mafi yawacin Yan siyasar nan dake sayen kuri’u, ana ganinsu ne cikin al’umma sau daya kacal a kowa ne shekaru hudu kuma suna zuwa ne rumfunan zaɓe su sayi kuri’u su tafi sai kuma bayan shekara hudu su dawo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram