Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya musanta rade-radin da akeyi yadawa da yayi na neman tikitin takarar musulmi da musulmi na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
A wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar Imo, Declan Emelumba, gwamnan ya ce babu wani lokaci da ya yi magana irin wannan.
Sanarwar ta ce Gwamnan ya jaddada cewa kada addini ya zama sanadin zabar dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar amma sai dai cancanta.
“Yaya wannan matsayi zai kai matsayin bayar da tikitin takarar shugaban kasa na Musulmi da Musulmi?” Kwamishinan ya tambaya.
Ya ci gaba da zargin wadanda suka bayyana a matsayin masu yin barna da karkatar da kalaman gwamnan.
“Gwamnan ya bayyana karara cewa babu wani bangare na Kundin Tsarin Mulki da addini ke da nasaba da zaben Shugaban kasa ko mataimakinsa,” in ji shi.
Ya ce gwamnan na Imo ya jaddada cewa jam’iyya mai mulki na neman tikitin da za ta fuskanci al’amuran mulki daidai gwargwado ba wai a yi maganar da za ta raba kan jama’a ba.