Da Ɗuminsa: Kotun Ƙoli Ta Bada Umarnin Amfani Da Hijabi A Makarantun Jahar Lagos

Kotun Ƙoli ta Najeriya ta tabbatar da damar da Musulmai mata ke dashi a Jahar Lagos na suyi amfani da Hijabi a makarantu, ba tare da cin mutunci, ko wulaƙanci ba.

Babbar Kotun ta bada umarnin ne a ranar Juma’a a Abuja.

Daga cikin waɗanda suka zauna Shari’ar akwai Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, da Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, Mai Shari’a John Inyang Okoro, da Mai Shari’a Uwani Aji, da Mai Shari’a Mohammed Garba, da Mai Shari’a Tijjani Abubakar, da Mai Shari’a Emmanuel Agim.

A yayinda guda huɗu suka bada umarni na yin amfani da Hijabi, guda biyu daga cikin su sun bukaci a fasa.

Babbar Kotun Jahar Lagos a watan Oktoba na Shekarar 2014 ta bada umarnin hana amfani da Hijabi a Makarantu, hukuncin da Kotun Daukaka kara ta warware shi a watan Yuli na Shekarar 2016.

A hukuncin data yanke tace hana ɗiyan musulmi amfani da Hijabi, musguna wa ce a garesu a Jahar Lagos.

Rashin amincewa da hukuncin, Gwamnatin Jahar ta ɗaukaka kara zuwa Kotun Ƙoli.

Ta sanya hana amfani da Hijabi a watan Ogusta na Shekarar 2018.

Amma a hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke, ta tabbatar da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na amfani da Hijabi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram