Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari
Dr Doyin Okupe tsohon Mai Tamakawa Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo akan Kafafen Yada Labaru, a ranar Juma’a yace shine abokin Takarar Dan Takarar Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi.
Okupe ya bayyana haka a ranar Juma’a a lokacin da gidan talabijin na Channels ya tattauna dashi, a cikin Shirin Siyasa A Yau wato- Politics Today.
Ya bayyana cewa, Jam’iyyar ta tura sunan sa ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC.
Okupe yace “yanzu Ina a matsayin Wanda zai yiwa Dan Takarar Jam’iyyar Labour Party mataimaki.
“Jam’iyyar Labour Party ta aike da suna na a matsayin Wanda zai yi Takarar Mataimaki.”
Jarida The PUNCH ta ruwaito cewa Tsohon Gwamnan Jahar Anambra ya amshi shaidar kasancewar sa Dan Takarar Jam’iyyar Labour Party biyo bayan samun nasarar sa a matsayin Dan Takarar da zai tunkari Babban Zaben Shekarar 2023 a Juma’ar data gabata.
Ya samu nasara a matsayin Dan Takarar Jam’iyyar na Shugaban Kasa a Babban taron Jam’iyyar daya wakana a Asaba, Jahar Delta a ranar 30 ga watan mayu na Shekarar 2022.