Karanta Sunayen Manyan Kwamandojin ISWAP Da Sojoji Suka Kashe

Karanta Sunayen Manyan Kwamandojin ISWAP Da Sojoji Suka Kashe

Ƙungiyar Ƴan Ta’addan ISIS sun fitar da sunayen Kwamandojin Ƙungiyar Ƴan ta’addan ISWAP da Sojoji suka hallaka.

Jami’an tsaron Najeriya haɗin gwiwa da Jami’an tsaron haɗin gwiwa sun hallaka ƴan ta’adda a wasu makonni da suka gabata.

Daily Trust ta bada rahoton yanda Dakarun Soji suka ƙaddamar da kisa ga mayaƙan ISWAP a tafkin Chadi da kuma Dajin Sambisa.

Sojoji dai sun yi ƙawanya a sansanin ƴan ta’addan, inda suka ragargaza mayaƙa sama da dubu 3,000 na ɓangaren Abubakar Shekau.

Wasu Mayaƙan sun shiga Ƙungiyar ISWAP bayan ɓangaren ƴan ta’addan sun hallaka Shekau a Shekarar data gabata.

A cewar bayanan sirri, Dakarun Sojin da ƴan ta’adda sun kasance sunyi musayar wuta wadda ta wuce sama da awanni uku.

A lokacin an kama Kwamandojin Ƴan Ta’addan guda biyu.

“An kama ƴan ta’adda guda biyu. A lokacin da aka bincike su, sun tabbatar da cewa, yanzu Abu Ikilima shike jagorantar sansanin su. Da Khayds (Gwamnoni) guda uku da Munzul (Kwamandoji) uku, da Nakib(Kwamanda) guda 1 na Boko Haram, inda aka kashe wasu da dama”, Inji majiya

A cikin bidiyon da Ƙungiyar ISIS ta fitar, ta ambaci sunayen Kwamandojin da ISWAP ta rasa

Abu Musab al-Yobawi
Abu Nu’man al-Amni
Abu Abdullah al-Barnawi
Abu ‘Ammara al-Barnawi
Abu Anas al-I’alami
Abdul Malik al-Barnawi
Abu Sufyan al-I’alami
Shaykh Abu Bakr al-Da’wi
Abu Usama Goneri
Abu Sa’d al-Ansari
Abu Jabbar al-Barnawi
Abu Anas al-Barnawi
Abu Abdul Rahman al-Katsanawi
Abu Maryam al-Gaidami
Abu Salman al-Ansari
Baka Goneiri
Abu Mustafa al-‘Askari
Farooq al-Barnawi
Abu Ahmad al-I’alami
Al-Qassim Al-Barnawi
Mustafa al-Barnawi
Abbas al-Ansari
Musa al-Ansari

Wannan labari na zuwa ne bayan an ɗorawa Ƙungiyar alhakin kai hari daya haddasa mutuwar masu bauta a Cocin Katolika ta Owo dake Jahar Ondo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram