An gurfanar da wata mai-gida, mai shekaru 53, Bukola Odusote a gaban kotu, bisa zargin haddasa rashin zaman lafiya bayan da mari ƴar-haya a jihar Legas.
Odusote ta bayyana a gaban kotun Majistare ta Ojo a kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da cin zarafi, barazana ta hanyar tsoratarwa, da kuma rashin zaman lafiya.
Sai dai ta musanta aikata laifukan a gaban Majistare L.K. Layeni.
Dan sanda mai shigar da kara, Dakta Simon Uche, ya shaida wa kotun cewa wacce ake tuhuma ta aikata laifin ne a cikin watan Maris a Bonny Bus Stop da ke kan titin Ojo-Igbede a jihar Legas.
Uche ya yi zargin cewa wacce ake zargin ta ci zarafin mai ƴar-hayarta, Helen Richman, ta hanyar gaura mata mari da kuma ture ta har ta faɗi ƙasa.
Mai gabatar da ƙarar ya ƙara da cewa wacce ake ƙarar ta takali faɗan ne bayan da ta hana mijin Helen, Kelvin Richman, ajiye motarsa a harabar gidan.
Ya gabatar da cewa wacce ake tuhuma ta kuma ci mutuncin Kelvin ta hanyar kiransa mai tsafi.
Laifukan da ake zargin ta da su sun ci saɓa wa sashe na 56,168 da 172 na dokar laifuka ta jihar Legas, na shekarar 2015.
Alkalin kotun ya bayar da belin wacce ake kara a kan kudi Naira 100,000 tare da tsayayyu biyu na daidai wannan adadi.
Ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 24 ga watan Agusta.