Miyagu Sun Sare Kan Zaɓaɓɓen Kansila Da Ɗan Uwan Sa A Benue

Wasu miyagu sun sare wa zababben kansila Paul Ojile da dan uwansa kai a gundumar Orokam da ke karamar hukumar Ogbadibo a jihar Benue.

Kansilan da dan uwan sa sun yi batan dabo ne a ranar alhamis amma an dawo dasu da safiyar ranar Juma’a.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, zababben kansilan da dan uwansa wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, sun kafa wani bangare na tawagar jami’an tsaro da tun farko suka je aikin ceto wani da aka sace a yankin.

Ojile dai yana jiran a kaddamar da majalisar ne a wata mai zuwa kafin rasuwarsa kwatsam.

Shugaban karamar hukumar Ogbadigbo, Prince Samuel Onuh, ya shaida wa wakilinmu cewa marigayin mafarauci ne wanda tare da abokan aikinsa suka shiga aikin tsaro domin dakile ta’addancin sace-sacen jama’a a yankin.

Onuh ya ce a cikin ‘yan kwanakin nan, an yi garkuwa da mutane da dama tare da na baya-bayan nan wanda ya faru a ranar Alhamis, inda ya kara da cewa a gaskiya ma’aikatan ceto sun kama wasu masu garkuwa da mutane biyu tare da kubutar da wani da aka yi garkuwa da shi kafin daga bisani su gano cewa mutane biyu daga cikinsu sun bace.

“An yi garkuwa da mutane a jiya (Alhamis); a zahiri a cikin kwanaki ukun da suka gabata, masu garkuwa da mutane sun addabi yankin, an yi ta yin garkuwa da mutane babu kakkautawa a karamar hukumar. Sun tashi daga wata al’umma a Owukpa, suka tafi Orokam; A kan hanyar su ne suka yi garkuwa da mutum guda.

“Zababben kansila da ke zaune a kauyen mafarauci ne. Shi kansa da dan uwansa da sauran mafarauta da kuma kungiyar ‘yan banga mai suna Operation Zenda (kayan ‘yan sanda) sun shiga dajin don ganin ko za su iya kubutar da mutumin da aka yi garkuwa da shi;

A lokacin da za su dawo ne a jiya suka lura biyu daga cikinsu sun bace amma sun samu nasarar cafke biyu daga cikin masu garkuwa da mutane. Da safiyar yau ne suka sake duba gawarwakinsu – zababben kansila da dan uwansa,” in ji shugaban.

Ya kuma ce, kungiyar “Operation Zenda ne suka kai masu garkuwa da mutane zuwa Makurdi.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai, SP Catherine Anene, ta shaida wa manema labarai a Makurdi cewa, ‘Operation Zenda ta kawo wadanda ake zargin zuwa Makurdi amma har yanzu ba ta samu cikakken bayani kan lamarin ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram