Yanzu-Yanzu: Majalisar Dokokin Jahar Kogi Ta Tsige Mataimakin Shugaban Ta Ahmed Muhammed
Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jahar Kogi Hon. Ahmed Muhammed an tsige shi.
A cikin wani zaman gaggawa daya wakana a zauren ta dake Lokoja a ranar Juma’a, ƴan Majalisun sun ƙalubalanci Ahmed Muhammed da wasu guda uku manyan Shuwagabannin Majalisar da rashin ɗa’a da amfani da ofishin su ba bisa ƙa’ida ba.
A Wani Ƙudiri da Enema Paul ya gabatar, Ɗan Majalisa Mai Wakiltar Dekina/Okura na Jahar, yace Ƴan Majalisu 17 duka sanya hannu na tsige Ahmed Mohammed tare da dakatar da wasu mutum uku a Majalisar.
An dai cire su daga ofishin su, kafin daga bisani aka dakatar dasu daga Majalisar, da suka haɗa da Shugaban Masu Rinjaye Hassan Balogun, da Mataimakin Shugaban masu rinjaye Idris Ndako, da Shugaban Masu tsawatar wa Hon. Edoko Moses Ododo.
Majalisar ta sanar da Alfa Momoh Rabiu, Ɗan Majalisa mai wakiltar Ankpa II a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Majalisar.
Sauran sabbin manyan Shuwagabannin Ƴan Majalisar sun haɗa da Hon. Mukhtar Bajeh a matsayin Shugaban Masu Rinjaye, Umar Isah Tanimu Mataimakin Shugaban masu rinjaye, da Enema Paul Mataimakin mai tsawatar wa, gami da Ahmed Dahiru a matsayin sabon Shugaban masu tsawatar wa.
Shugaban Majalisar Prince Mathew Kolawole tun da farko ya sanar da rushe dukkanin wani kwamiti a majalisar.
Kafin a fara zaman sauke Su, an hangi dandazon Jami’an tsaro a Majalisar, wanda ya haɗa da ƴan Sanda, da ƴan Sibil Difens, da DSS.
Ahmed Muhammed da aka tsige ya kasance Ɗan Majalisa ne mai Wakiltar Akpa I a Majalisar Dokokin Jahar Kogi.
Ƴan Majalisu 17 daga cikin 25 suka halarci tsige Shuwagabannin Majalisar.