Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutane 5 A Jahar Anambra

Akalla mutane biyar ne ake zargin ‘yan bindiga ne da ba a san ko su wanene ba suka hallaka,

Lamarin ya faru ne yayin wata arangama da ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, a Ihiala, jihar Anambra.

Wani ganau da ya ga motar Hilux dauke da gawarwakin ‘yan bindigar daga cikin garin, ya ce mutane sun yaba wa ‘yan kungiyar ta IPOB da ke harbin iska yayin da suka nufi hanyar Onitsha zuwa Owerri.

Mutumin ya ce: “Gaskiya ne. Lamarin dai ya faru ne a kauyen Akwa da ke Ihiala a yayin wani artabu tsakanin kungiyar ta IPOB da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba.

“’Yan bindigar suna da sansani a wani wuri da ake kira Oseakwa inda suka addabi Ihiala, Okija, Uli da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da su.

Haka kuma a ranar Juma’ar da ta gabata wasu mutane da ake zargin ‘yan kabilar Ebubeagu ne sun yi arangama da ‘yan bindiga a Ihiala a yayin da ake bikin jana’izar, duk da cewa ba a samu asarar rai ba.

A cewar ganau, bayan arangamar, sai da aka soke binne gawar sannan aka mayar da gawar zuwa dakin ajiyar gawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, PPRO, Mista Tochukwu Ikenga ya shaida wa Vanguard cewa har yanzu bai samu rahoton faruwar lamarin Ihiala ba.

A kwanakin baya ne dai a cikin Ihiala, wasu ‘yan daba suka kona wani katafaren gida da ke kusa da kasuwar Aforigwe a kauyen Ubahuekwem bisa zarginsu da gayyatar ‘yan sanda bayan da mutumin ya biya ‘yan bindigar domin su ba shi tsaro a wani biki a harabar sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram