An Ƙone Ɓarawon Waya A Jahar Bayelsa

 

Wasu ɓata gari a ranar Asabar sun ƙone wani da ake zargin Ɓarawo ne a Yenagoa, Babban Birnin Jahar Bayelsa.

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Kwastam dake Biogbolo-Epie ta kan Babbar Hanyar Isaac Boro.

Wanda aka ƙonan da har yanzu ba’a samu bayan sa ba, an kama shi da laifin satar waya da ake zargin daga wani mutum na daban.

Matashin da ake kyautata zaton yakai shekaru 30, yana ɗaya daga cikin wata tawaga ta mutum 3 da suka ƙware da amfani da Keke Napep wajen yiwa mutane sata.

Mutum biyun dai sun tsere, a yayinda Al’umma suka kama shi, biyo bayan ihu da akayi wanda ya sanya aka gane su, tare da kama su.

A lokacin da wakilin majiyar mu ya ziyarci, har a lokacin aka hayaƙi da ƙura daga gawar wanda aka ƙona da taya.

Haka zalika, an hangi kimanin Ƴan Sanda 4 a saman mota a wurin, da Ɗumbin mutane suna duba ƙonanniyar gawar.

Wasu shaidun gani da ido sun yi zargin cewa yana ɗauke da bindiga ƙirar Ak-47 a lokacin da mutane suka kai mashi hari, inda suka ƙwace bindigar da tsiya, tare da sanya mashi taya a wuyan sa, gami da kunna mashi wuta da Fetur.

Wani daga cikin wanda suka aikata lamarin, daya buƙaci a sakaye sunan sa yace “ya saci waya ne mai tsada. Su uku ne a cikin Keke Napep. Yana riƙe da Ak-47, inda sauran suka riga, shi aka kama shi.

“Mutane sun kwace bindigar daga gareshi, tare da sanya mashi taya da ƙona shi. Naji ance budurwar sa na wurin, kuma tace sai da ta gargaɗe shi kada yaje satar, amma yaje. Kuma mutane ne suka ƙona shi bayan sun kira ƴan sanda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram