Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyya Mai Alamar kayan marmari NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, a halin yanzu suna tattaunawa da Takwaran sa Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar Labour Party Peter Obi.
Akwai yuwuwar Kwankwaso da Obi, su haɗa kansu domin tunkarar Zaɓen Shekarar 2023, tsakanin NNPP da Labour Party.
Ya bayyana haka ne, a lokacin da yake tattaunawa da Sashen BBC Hausa.
Kwankwaso yace “muna tattaunawa da Peter Obi, akwai kwamitin da yana aiki akan maganar haɗa kai dashi, sannan kuma Yan uwa da abokai suna buƙatar suga munyi hakan.
Ya nuni da cewa, Manufar yin hakan zaiyi amfani ne musamman ganin Jam’iyyar APC da Jam’iyyar PDP, basu sanya Dan kabilar Igbo a matsayin Ɗan Takarar mataimakin shugaban kasa.
A ranar Juma’a ne, Obi ya fitar da sunan Tsohon Mai taimakawa Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo akan Kafafen Yada Labaru, Doyin Okupe a matsayin mataimakin nasa.