EFCC Ta Kama Wani Ɗan APC  Da Siyan Ƙuri’a A Zaɓen Ekiti

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a ranar Asabar, sun kama wani da ake zargi da siyan kuri’u a jihar Ekiti a yayin da ake fara zaben gwamnan jihar.

Jami’an EFCC sun kama wanda ake zargin dauke da buhun kudi a yayin da ake “tantance masu zabe.”

Wanda ake zargin, wakilin jam’iyyar APC mai mulki ne, an tsare shi a makarantar Ola Oluwa Grammar School da ke kan titin Ilawe na garin Ekiti babban birnin jihar.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta gargadi masu kada kuri’a gabanin zaben kan siyan masu kada kuri’a.

INEC ta yi gargadin daukar tsauraran matakai kan bai wa masu kada kuri’a kudi.

Hukumar ta bayyana hakan ne a lokacin da take bayyana hadin gwiwarta da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ICPC, a ranar Juma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram