Gwamna Matawalle Ya Bada Hutun Sati Guda Ga Ma’aikata Don Yin Katin Zaɓe A Jahar

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle ya ayyana mako mai zuwa daga Litinin zuwa Juma’a, (20 ga Yuni zuwa 24 ga Yuni, 2022) a matsayin makon da ba aiki don baiwa jama’a da ma’aikatan jihar damar zuwa yankunansu da kuma karbar katin zabe na dindindin, (PVC).

Gwamnan ya umurci dukkanin kwamishinonin da masu ba da shawara na musamman da sakatarorin dindindin da sauran masu rike da mukaman gwamnati da jami’an jam’iyya da sarakunan gargajiya da su sanya ido tare kan yadda ake gudanar da rajistar masu kada kuri’a a fadin jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar kwamishinan yada labarai na jihar, Honorabul Magaji Dosara ya bai wa manema labarai a jihar.

A cewar sanarwar, ana sa ran duk wanda ya haura shekaru 18 zai shiga cikin wannan aiki, yana mai cewa hakkinsu ne da kundun tsarin mulki ya ba su na zaben shugabanninsu.

Gwamna Matawalle ya yi kira ga jama’a da su yi rajistan kada kuri’a don kada su koka daga baya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram