Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa tace mambobin Ƙungiyar ba mabara ta bane ba, kuma tsaida Albashin su da Gwamnati tayi, bazai sanya su janye yajin aikin da suke yi ba.
Shuwagabancin Ƙungiyar ya kuma yabawa Mambobin Ƙungiyar dasu tsayu tsayin daka da Ƙungiyar, duk da irin wahalhalu da aka sanya wa iyalan su, a dalilin dokar Babu Aiki babu Albashi da Gwamnatin Tarayya ta sanya a gare su.
Biyo bayan kasawar Gwamnati na cika wasu bukatun Ƙungiyar, ASUU a ranar 14 ga watan Fabrairu na Shekarar 2022 ta sanar da shiga Yajin aikin gargaɗi, inda ta bishi da wasu makonni 8, kafin daga bisani ta tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani.
Cigaba da wannan yajin aiki ya sanya Gwamnatin Tarayya ta sanya Dokar Babu-Aiki-Babu-Biyan-Albashi, kamar yadda Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan yi Dr. Chris Ngige ya bayyana cewa hakan na dai-dai da bin Dokar aiki ta sashe na 34.
Duk da wasu buƙatun Ƙungiyar ana cigaba da tattaunawa akansu, Shugaban Ƙungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana fatan cewa ƙungiyar na kan turbar samun nasara.
Ya yi nuni dacewar, matsayar da Ƙungiyar ta tsayu a kanshi ya sanya, Gwamnati ta shiga zauren tattaunawa dasu.
Yace “a yayinda muke cigaba da neman haƙƙin mu, muna yabawa Mambobin Ƙungiyar da jajircewa da haƙuri domin ɗorewar cigaban sashen Jami’o’i a Ƙasar mu”