Ɗan Takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Social Democratic Party (SDP) sun lashe rumfunan zabensu a zaben gwamnan Ekiti da ke gudana.
Yayin da Abiodun Oyebanji na APC ya samu kuri’u 81 a Ward 3, Igede Ekiti, dan takarar Peoples Democratic Party (PDP), Bisi Kolawole, ya samu kuri’u 23 yayin da Oni ya samu kuri’u 30.
Kimanin masu kada kuri’a 140 ne aka amince da su daga cikin masu kada kuri’a 367 da suka yi rajista a sashin.
A ward 2 unit 6, dake Ifaki Ekiti, inda Oni ya kada kuri’a, SDP ta samu kuri’u 218.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Oni wanda ya kada kuri’arsa da misalin karfe 11 na safe ya bayyana rashin jindadinsa kan yadda ake siyan kuri’u a zaben gwamna da ke gudana a jihar.
Abokin hamayyarsa, ya samu kuri’u 15, yayin da Kolawole ya zo na biyu da kuri’u biyu