Ƴan Bindiga Sun Sace Tsohon Sakataren Ƙungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya

Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari

Wasu Ƴan Bindiga sunyi Garkuwa da Tsohon Sakataren Ƙungiyar Wasan Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya Ahmed Sani Toro.

Rohoto ya bayyana cewa, sun yi garkuwa da Tsohon mataimakin kocin Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Golden Eaglets, Garba Iliya, akan hanyar Abuja zuwa Jos, a daren jiya.

Sun kasance dai Suna kan hanyarsu ta komawa Bauchi, bayan halartar bikin Ɗan Gidan Tsohon Shugaban Wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya, Alhaji Aminu Maigari, a garin Abuja wanda akayi ranar Juma’a.

Shugaban Kungiyar Ƙwallon kafa na Bauchi, kuma mafi kusa da wadanda akayi garkuwa dasu, ya bayyana cewa, masu garkuwar har yanxu basu tuntuɓi iyalan nasu.

Ya Ƙara da cewa, “gaskiya ne anyi garkuwa dasu a dai-dai Ryom a Jahar Filato, lokacin da suke kan hanyar dawowar su Bauchi daga Abuja.

“Sun halarci Ɗaurin auren Ɗan Gidan Alhaji Aminu Maigari a Babban Masallacin garin Abuja a ranar Juma’a.

“Na tuntuɓi iyalan nasu, sun kuma shaida Mana cewa har yanxu masu garkuwar basu ne mesu ba.

“Muna masu addu’a kuma muna fatan Allah ya kawo Mana sauƙin wannan hali da muke ciki, Allah kuma yasa a sako su lafiya”, Inji shi.

Ahmed Sani Toro, Shine Tsohon Kwamishinan Wasanni na Jahar Bauchi, kuma Tsohon Ɗan Majalisar Wakilai karo na daya, ya kasance Babban Sakataren Ƙungiyar Wasan Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya daga Shekarar 1993 zuwa 1999.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram