Ƴan Sanda Sun Kama Wata Da Laifin Bautar da Yara A Jahar Imo

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta tabbatar da cafke wata mata mai suna Victoria Nwosu ‘yar shekaru 26 da haihuwa, bisa zargin cin zarafi da kuma bautar da wasu ‘ya’ya guda uku.

Wani faifan bidiyo wanda ya bazu a yanar gizo inda aka ga kananan yara uku an daure su da sarka aka yi musu azaba ta ka da ta jiki.

Wani mazaunin yankin da abin ya faru, wanda ya yi faifan bidiyon, ya yi kira ga kungiyoyi da su kawo agajin yaran.

Daga bisani, kungiyar lauyoyin mata ta kasa da kasa reshen jihar ta shiga shirin daukar wani mataki, lamarin da ya kai ga cafke matar da mijinta.

Da yake tabbatar da kama matar, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya ce an kubutar da yaran ne kuma tawagar likitoci ta kai musu dauki.

Ya bada tabbacin za a gurfanar da ma’auratan a kotu a karshen binciken.

”A kokarin ceto yaran ne jami’an ‘yan sandan suka garzaya da su asibitin gwamnati da ke kusa da su inda aka yi musu magani aka sallame su.

Sai dai daga baya an mika su ga gidan marayun da gwamnati ta amince da shi, inda za a kula da su har zuwa lokacin da za a gano mahaifiyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram