Dangote, Ƴan Kasuwa Sun Tara Biliyan 15 Domin Gina Asibitin Matan Sojin Ruwa

Hamshaƙin Ɗan Kasuwar nan kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, da wasu manyan Ƴan Kasuwa a Ƙasar, sun tara Naira biliyan 15 domin gina Asibiti mai cin gado 200, da Ƙungiyar Matan Sojojin Ruwa (NOWA) ta ƙirƙira.

Daily Trust a ranar Lahadi ta bada rahoton cewa Uwargidan Shugaban Ƙasa Hajiya Aisha Buhari, a ranar Litinin ta ɗora harsashin ginin Asibitin, tana mai jaddada cewa cewa, gina Asibitin nada nufin kula da Matan Sojoji da Ƴaƴan su, da kuma Al’umma mazauna Karkara.

Sauran ƴan kasuwa da suka haɗa da ɓangaren Mai da Iskar Gas, da ɓangaren gini, da Banki, da wasu manyan Ma’aikata, tuni sun bada gudunmawar su ga aikin.

Da take jawabi a Abuja a bikin tara kuɗin, Shugabar Ƙungiyar Hajiya Nana-Aisha Gambo tace Matan Sojoji a shirye suke domin samar da isassar kiwon lafiya ga Mata da Ƙananan Yara.

Tace ” ya zama dole mu fara wannan aikin a matsayin wata hanya ta samun isasshiyar lafiya ga Iyalan Matan Sojoji a Babban Birnin Tarayya da Ƙasa baki ɗaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram