Majar LP-NNPP: Akwai Yiwuwar Kwankwaso Ko Peter Obi, Wani Ya Zama Mataimaki A Takarar Su

Sakataren Yaɗa Labaru na NNPP Dr. Agbo Major yace tattaunawa ta haɗin gwiwa tsakanin Jam’iyyar Labour Party da Jam’iyyar yana tafiya yanda ya kamata, kuma Dr. Rabiu Kwankwaso, wanda shine Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na NNPP zai iya karɓar Peter Obi a matsayin abokin takarar sa.

Obi shine Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar Labour Party, Kuma tuni ake ta yawo da jita-jitar cewa zai iya yin maja da Kwankwaso a matsayin Abokin Takara.

Da aka tambaye shi, akan ya tabbatar da batun yin Maja, yace tattauna na cigaba da wakana a tsakanin su.

Yace Kwankwaso ko Obi, wani daga cikin su zai amince ya zama Mataimakin wani a Takarar.

Major da yayi jawabi da Daily Trust ta hanyar wayar salula yace “daga lokacin da muka kammala, ƴan Najeriya zasu yi farin ciki, duk abinda aka sanar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram