Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari
Ƴan Sanda sun yi nasarar kama wani Ɗan Bindiga bayan ya samu munanan raunika tare da bindigar sa ƙirar AK 47, a lokacin wani musayar wuta, tsakanin sa da Jami’an tsaro da Ƴan ta’adda a Ƙaramar Hukumar Gummi dake jahar Zamfara.
Kamar yadda Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan, SP Mohammed Shehu ya fitar a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa, Jami’an Ƴan sanda haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro sun fafata da Ƴan ta’addan na kusan awanni huɗu, wanda a dalilin haka ne suka yi nasarar kama ɗaya daga cikinsu, da suka yiwa munanan raunika, tare ƙwato bindigar sa ƙirar AK 47.
Shehu ya Kara da cewa, “a ranar 19 ga watan yunin Shekarar 2022, Ƙwararrun Jami’an Ƴan sanda da aka tura Gummi/Bukkuyum, sun samu kiran gaggawa cewa, Ƴan ta’adda akan Babura sun shiga garin Saran Gamawa da garin dake makwabtaka dashi na ƙauyukan Unguwar Mata, da niyyar Kashe mutane da ɗaukar al’ummar yakin.
“Rundunar Ƴan sanda haɗin gwiwa da Ƴan Ƙungiyar Ƴan sa kai, sun haɗa wata tawaga, tare da yin muyasar wuta da Ƴan ta’adda na tsawon awanni.
” A dalilin haka ne, ɗaya daga cikin ƴan ta’addan ya samu mummunan rauni, a sa’ilin da jami’an sukayi nasarar samun bindagar sa mai kirar AK 47.
” Da yawa daga cikinsu sun ruga cikin daji da mummunar raunuka da harbin bindiga yayi masu.”
Kwamishinan Ƴan Sandar Jahar, CP Ayuba N. Elkanah, ya yabawa Jami’an tsaron da irin jajircewar su, da kira a garesu su Ƙara ƙaimi wurin kare rayukan Al’umma da dukiyoyinsu, dake a Faɗin Jahar.