Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya tashi zuwa kasar Morocco a ziyarar aiki ta mako guda a kasar.
Wata sanarwa da ta fito daga fadar Sarkin a ranar Litinin ta bayyana cewa ziyarar ta biyo bayan gayyatar Sarki Mohammed VI ne.
Ya ce a yayin ziyarar, Sarkin zai gudanar da wasu ayyuka a hukumance da hukumomin kasar Morocco, ciki har da ganawa da ‘yan kasuwa da shugabannin addinai.
“Alhaji Aminu Ado Bayero da tawagarsa za su kuma ziyarci wasu manyan biranen kasar Morocco kamar su Marrakech, Casablanca, Rabat, Tangier da kuma birnin Fes mai tsarki da dai sauransu.
“Ziyarar za ta kare ne da ziyarar ban girma ga Sarki Mohammed VI, wanda ake sa ran sarkin zai dawo Najeriya a farkon mako mai zuwa,” in ji sanarwar.
A cewar sanarwar, wadanda ke cikin tawagar Sarkin sun hada da Alhaji Ahmed Ado Bayero, Sarkin Dawakin Tsakar Gida da Hakimin Kumbotso, Ambasada Ahmed Umar.
Sauran sun hada da Dan Malikin Kano, Alhaji Ahmed Ibrahim Matawalle, Talban Kano, Alhaji Magaji Galadima, Kachallan Kano da gungun jiga-jigan ‘yan kasuwa daga ciki da wajen kungiyar ma’adinai da noma ta Kano