Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar na fama da matsanancin rashin lafiya, kamar yadda jaridar Thisday ta ruwaito.
Mai yiwuwa Janar din soja mai ritaya ya na fama da cutar hawan jini.
Rahotanni sun bayyana cewa an fitar da Abubakar daga Najeriya kimanin makonni uku da suka gabata domin yin jinya.
Da farko dai an dauke shi zuwa Dubai a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) amma yanzu yana wani asibiti a kasar Ingila (UK).
Abubakar ya samu rakiyar matar sa da kuma uwargidan tsohon shugaban kasa, Mai shari’a Fati Abubakar.
Surukin sa kuma gwamnan Neja, Abubakar Bello ya bar kasar bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC ya kai masa ziyara.
An kuma tattaro cewa shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) yana cikin koshin lafiya yayin da likitoci ke ci gaba da sa ido a kansa.