Ƴan Bindiga Sun Saki Dagacin Ƙauyen Bauchi, Da Ɗan Sa

Ƴan Bindiga sun saki Dagacin Ƙauyen zira dake Ƙaramar Hukumar Toro a Jahar Bauchi, Yahaya Abubakar tare da Yaron sa, Habibu.

An sake su ne, a safiyar ranar talata, kuma tuni sun koma cikin iyalan nasu.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, Ƴan bindigar sun shiga kauyen zira da misalin Ƙarfe biyu na dare a ranar Asabar, inda suka yi garkuwa da Dagacin da kuma yaron nasa.

Babu tabbacin cewa, iyalan Dagacin sun biya kuɗin fansa kafin a sako su.

Jami’in Tulda da Jama’a na Rundunar, SP Ahmed Wakil, ya tabbatar wa Ƴan jarida a Bauchi cewa, an sako su a ranar talata .

Ya Ƙara da cewa, “a yau Dagacin Ƙauyen zira da yaron sa sun samu ƴancin dawo wa, kuma kowane nan su na cikin ƙoshin lfy.

Wakil bai bada wani bayani baya ga wanda ya bada, dangane da lamarin.

Majiyar Wakilin mu ya bada rahoton cewa, sun samu dawo ne bayan an sako Tsohon Sakataren Ƙungiyar Wasan Ƙwallon kafa ta Najeriya, Alhaji Sani Toro da Tsohon mataimakin kocin kungiyar wasan kwallon kafa ta Super Eagles Garba Yila da kuma wani mutum, sun samu ƴancin dawo wa gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram