An Kashe Mutane 5, Goma Sun Ɓace A Wani Sabon Hari Da Aka Kai Benue

Akalla gawarwaki biyar ne aka samu a ranar Talata bayan da wasu ‘yan ta’adda suka sake kai wani sabon hari a kan al’ummar karamar hukumar Guma da ke jihar Benuwe.

Jaridar Daily Trsu ta gano cewa mutane 10 sun bace yayin da aka tura jami’an bincike don tseratar da wadanda aka yi garkuwa da su.

Shugaban karamar hukumar Guma, Caleb Aba, ya shaida wa wakilin majiyar jaridar Dimokuraiyya ta wayar tarho cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a unguwar Mbagwen amma an sanar da shi da yammacin ranar Talata.

Aba ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da dillalan katako wadanda suka je da yammacin ranar Litinin domin kai katakon da suka sare daga dajin Mbagwen, wata al’umma da ke kusa da Yelewata a Guma.

“Lamarin ya faru ne a jiya (Litinin) da yamma inda wasu ‘yan kasuwa masu sayar da katako suka je dauko katakon su daga dajin.

“(masu sana’a) sun yi lodin katako kuma suna kan hanyarsu ta dawowa lokacin da aka kai musu hari. Sun kasance 15 ne lokacin da lamarin ya faru.

Ya zuwa yanzu dai an gano gawarwaki biyar. Ba a ga wasu mutane goma ba. Ba mu sani ba ko an kashe su ko an tafi da su. Ana neman su ne yayin da nake magana da ku,” in ji shugaban.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta ce ba ta da wannan labarin, inda ta ce tana halartar wani taron bita a wajen jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram