Jaridar The Nation ta ambato Sakataren IPMAN, reshen Legas Akeem Balogun na cewa ”lura da yadda kasuwar take a yanzu, babu yadda za a yi mu sayar da mai kasa da naira 180 a duk lita”.
Ya kara da cewa ”duk wani mamba da wata hukuma ta hana yin haka ya yi gaggawar sanar da uwar kungiya.”
An shafe watanni ana wahalar mai a Najeriya, musamman a manyan biranen kasar da suka hada da Abuja da Lagos.
IPMAN reshen na jihar Legas, ta ce rufe gidajen man wasu mambobinta ya kara haifar da dogayen layuka musamman a Lagos da Akure da Ado-Ekiti da Abeokuta da Jos