Ka Fara Gyara Mana Munanan Hanyoyi, Kafin Kabar Ofis – Mutanen Warri Ga Okowa

Yayin da gwamnatin Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ke kara tabarbarewa, mazauna garin Warri na ci gaba da kokawa kan halin rashin kyawu na wasu titunan birnin mai arzikin man fetur, inda suka yi kira ga gwamnan da ya gyara su kafin ya bar ofis.

Mazauna yankin sun ce sun sha fama da wahalhalu da ba za a taba mantawa da su ba tsawon shekaru bakwai da suka gabata, sakamakon munanan hanyoyin da suka shafi tattalin arzikin yankin, yayin da kasuwancin su ke ci gaba da koma-baya, sakamakon rashin kyawun hanyoyin.

Wani mazaunin unguwar da ya bayyana sunansa Mista Okonedo Andrew, mazaunin wari mai lamba 12 Ojugo, daura da titin Giwa-Amu, Warri, ya shaida wa wakilinmu cewa, sun sha wahala ne saboda rashin hanyar tun lokacin da ya hau mulki.

Okonedo ya ce a lokacin da ya hau kan mulki bai san cewa titin ya yi muni ba saboda ya shiga lokacin noman rani.

Ya ce a duk lokacin damina a kan samu ambaliya a kan titi, lamarin da ya sa wasu mazauna yankin ba su da wani zabi illa su nemi mafaka da ‘yan uwansu a wani wurin har sai an gama damina.

Okonedo ya ce, “Mun rubuta wa gwamnatin jihar wasiku da dama ta hannun kwamishinan ayyuka amma duk abin ya ci tura. Abin da suke ta fada mana tsawon shekaru bakwai da suka wuce shi ne nan ba da dadewa ba za su fara aikin titin.

Mu da muke zaune kuma muna da shaguna a nan, ba za mu iya yin kasuwanci a lokacin damina ba, domin titin gaba daya ya cika da ruwan.

Ni mai dinki ne kuma ina da kantina a nan amma saboda munin hanyar yasa abokan ciniki ba sa zuwa saboda duk wurin ya cika da ruwa,” inji shi.

Wani mazaunin unguwar Mista Kesiena Omoyibo da ke zaune a titin Ginuwa 22 a garin Warri ya bayyana cewa sama da shekaru takwas suna fuskantar ambaliyar ruwa a titin, inda ya ce a lokuta da dama ambaliyar ta shiga gidajensu a duk lokacin da aka yi ruwan sama.

Ya ce, “Wannan hanya ta kasance haka tsawon shekaru kuma gwamnati ta ki ta zo ta gyara mana. Dole ne mu nade wando mu ja takalmanmu a hannunmu duk lokacin da za mu fita da kuma dawowa gida.

“Don Allah Okowa ya kawo mana agaji saboda muna shan wahala. Mutane suna kiran Okowa Jagoran Hanya amma ba mu ji tasirin wannan sunan a wannan titi ba. Ya zo ya gyara mana wannan hanya kafin ya bar mulki mu ce ya yi mana wani abu,” inji shi.

Hanyoyi da dama a cikin birnin mai arzikin man fetur da suka hada da Effurun Roundabout, Sokoh Estate, First Marine Gate, Etuwewe, da Uti da dai sauransu suna cikin mummunan hali.

Yanzu haka dai mazauna yankin sun roki gwamnatin jihar karkashin jagorancin Sanata Ifeanyi Okowa da ta kawo musu dauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram