Majalisar Wakilai Zata Binciki Kayayyakin Da Ake Amfani Da Su Na Tsaftace Masai A Kasuwannin Najeriya

Kudurin fara binciken kayayyakin da ake sayarwa wadanda ake amfani dasu wajen wanke bayan gida da sauran kayan gida a kasuwanni ya biyo bayan kudirin da dan majalissa Sergius Ogun daga jihar Edo ya gabatar.

A cikin kudirin nasa, Ogun ya bayar da hujjar cewa magungunan tsaftace bayan gida irin su harpic da hypo da ake amfani da su a yawancin gidaje a Najeriya ba su da inganci, rashin inganci kuma suna barin abubuwa da yawa da ake so a tsaftace su daga datti.

Dan majalisar ya nuna damuwarsa kan yadda tallar da gaskiyar lamarin ke cin karo da juna, don haka kamfanonin ke yaudarar ‘yan Najeriya.

“Duk da rashin ingancin wadannan magungunan tsabtace bayan gida, akwai tallace-tallace da dama da gidan talabijin ke daukar nauyinsu da ke yaudarar jama’ar da ba su ji ba gani, wadanda ke dogaro da irin wadannan bayanan tallace-tallacen don yin sayayya;

Ya lura cewa “Sashe na 17 (e) na dokar hukumar gasa ta tarayya da kare masu amfani da kayayyaki ta shekarar 2018 ta baiwa hukumar ikon gudanar da binciken da ake ganin ya zama dole ko kuma abin da ake bukata dangane da al’amura da ke cikin dokar.

Don haka majalisar ta bukaci mataimakin shugaban hukumar FCCPC da ya gurfana a gaban kwamitin kasuwanci don tabbatar da kasancewar baragurbin garaya, da sauran magungunan da ba su da inganci a kasuwa ko akasin haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram