Sanatoci 3 Sun Kara Sanar Da Ficewa Daga Jam’iyar APC Mai Mulki

 

Sanatoci uku na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun yi murabus daga mukaminsu a jam’iyya mai mulki.

‘Yan majalisar sun hada da Sanata Ahmad Babba Kaita (Katsina ta Arewa), Lawal Yahaya Gumau (Bauchi ta Kudu), da Francis Alimikhena (Edo ta Arewa).

Yayin da Babba Kaita da Alimikhena suka sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, Gumau, a daya bangaren kuma ya koma jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Sanarwar murabus din nasu da sauya shekar nasu na kunshe ne a cikin wasiku daban-daban guda uku da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zaman majalisar a na yau Talata.

Wasikar Babba Kaita ta ce, “A matsayina na Sanata mai wakiltar mazabar Katsina ta Arewa, na rubuta ne domin sanar da ku cewa na fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da shelanta rajista na a jam’iyyar Peoples Democratic Party wato PDP.

“ Ficewara daga jam’iyyar APC ta samo asali ne daga yadda gwamnatin jihar da shugabannin jam’iyyar a jihar Katsina suka mayar da wasu daga cikinmasu ruwa da tsaki saniyar ware, inda kananan mutane irina ba sa samun dama a siyasar jihar.

“Tun daga nan na kasance cikin farin ciki da karbuwa a cikin jam’iyyar PDP a jihar Katsina.” inji shi

A nasa bangaren, Sanata Alimikhena, ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC ne sakamakon “rikicin da ke ci gaba da dagula al’amura da dama da suka durkusar da jam’iyyar APC, musamman a gundumarsa ”

Sauya shekar da ‘yan majalisar uku suka yi ya rage yawan Sanatocin APC daga 70 zuwa 67 a majalisar dattawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram