Sanata Umaru Al-Makura, jigo a jam’iyyar APC daga Nasarawa ya ce zabin Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki shi ne mafi alheri ga Najeriya.
Al-Makura, mamba a kungiyar ‘Think-Think of Tinubu for President’, ya yi wannan ikirarin ne a wata ganawa da kungiyoyin goyon baya daban-daban daga jihar Nasarawa domin neman dan takarar a ranar Talata, kamar yadda NAN ta ruwaito.
Tsohon gwamnan ya kira Tinubu a matsayin babban jarumi a dimokuradiyya wanda tare da sauran masu kishin kasa suka yi gwagwarmayar wajan tabbatar da dimokuradiyya a lokacin da kasar nan ta fada cikin yanayu mafi hadari.
Ya ce Tinubu ya sauya jihar Legas a matsayin gwamnanta daga 1999 zuwa 2007 wanda har tazama yadda take a halin yanzu.
“Tinubu zai yi abun da ya dace don tabbatar da doka da oda wanda ya canza jihar Legas idan aka zabe shi a zaven hekarar 2023.
Ya kara da cewa, “Ya kashe kudin sa don tabbatar da mulkin dimokaradiyya a kasar nan kuma abu ne da ya dace a zabi irin wannan a matsayin shugaban kasa,” in ji shi.