INEC Zata Ɗauki Masu Buƙata Ta Musamman Ma’aikatan Zaɓe

Kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Osun, Farfesa Abdulganniy Rabi, yace zasu dauki masu bukata ta musamman domin aiki tare dasu.

Farfesa Raji yace masu bukatar ta musamman zasu kasance cikin rukunin Ma’aikatan wucin gadi da hukumar zata dauka, domin aikin zaben Gwamnan jihar da za a gudanar.

INEC dai ta shirya gudanar da zaben Gwamnan jihar Osun ne, ranar 16 ga watan Yuli Mai kamawa.

Raji ya sanar da wannan albishirin ne lokacin da yake ganawa da shugaban kungiyar masu bukata ta musamman na sanatoriya jihar a Osogbo.

Ya kara da cewa wannan kokarin da zasu zai taimaka wajen shigar da masu bukata ta musamman cikin al’umma yadda ya kamata, tare da kawar musu da zargin kyamar su da suka tunani.

Da yake nasa jawabin daraktan cibiyar dimokuraɗiyya a Najeriya, Me Steven Snook, ya bukaci INEC ta tabbatar da cewa ta dauki masu bukata ta musamman din kamar yadda ta sanar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram